Salwa RTV
Kaitsaye

GWAMNATIN JIHAR KATSINA TA TAYA YAN ASALIN JAHAR MURNAR LASHE GASAR IBERCUP.


 GWAMNATIN JIHAR KATSINA TA TAYA YAN ASALIN JAHAR MURNAR LASHE GASAR IBERCUP. 
              
Gwamna Radda Ya Taya 'Yan Wasan Kwallon Kafa 'Yan Asalin Jihar Katsina Murnar Lashe Gasar IberCup Estoril 2026.
 da aka gudanar a birnin Lisbon na ƙasar Portugal.

Gwamnan ya bayyana nasarar a matsayin abin alfahari ga Jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya, yana mai cewa ta nuna ƙwarewa, jajircewa da hazaƙar matasan jihar.

Moonluck FA ta lashe kofin ne bayan doke GD AMB Football Club a wasan ƙarshe, yayin da tun da farko ta doke ƙungiya daga Guinea-Bissau da ci 1–0, inda Sadiq Salihu ya ci ƙwallon da kaisu ga nasara.

Gwamna Radda ya yabawa masu huras da 'yan wasan,  da shugabannin makarantun ƙwallon kafa bisa ƙoƙarinsu, tare da jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa ci gaban wasanni da bunƙasa hazakar matasa domin su ci gaba da ɗaukaka sunan Katsina da Najeriya a duniya.

Ya kuma buƙaci 'yan wasan su ci gaba da kasancewa masu ƙwazo, ladabi da jajircewa, yana mai tabbatar musu da cikakken goyon bayan gwamnatin jihar wajen haɓaka harkokin wasanni.

Ibrahim Kaula Mohammed
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Katsina
06 Yuli, 2026
           ..Salwa Rtv Katsina.. 

Post a Comment

Previous Post Next Post