DAGA GIDAN GWAMNATI, KATSINA
SANARWAR MANEMA LABARAI
EKITI 2026:
Gwamna Radda Ya Taya Gwamna Oyebanji Murnar Samun Nasarar Lashe zaben da ya gudana a wannan makon,
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya taya Mista Biodun Abayomi Oyebanji, Gwamnan Jihar Ekiti, murnar sake lashe zaɓen gwamna karo na biyu.
A cikin saƙon taya murnarsa ga Gwamnan Ekiti, Gwamna Radda ya bayyana cewa wannan nasara wata babbar alama ce ta amincewa da jama'ar Ekiti suka nuna ga shugabancinsa da kuma ayyukan da ya gudanar a wa'adinsa na farko.
Ya ce:
"Wannan ita ce mafi gaskiyar tantancewar da shugaba zai iya samu. Yana nuna cewa jama'a sun ga abin da ya yi. Sun auna sakamakon ayyukansa. Kuma sun yanke hukuncin cewa ya cancanci a ba shi wata dama akaro na biyu.
A tsarin dimokuraɗiyya, wannan hukunci na jama'a ya fi kowace lambar yabo ko yabon da za a yi wa shugaba muhimmanci."
A madadin gwamnati da al'ummar Jihar Katsina, Gwamna Radda ya miƙa sakon taya murna ga Gwamna Oyebanji tare da yi masa fatan samun nasara a wa'adinsa na biyu.
Ya kuma yi addu'ar cewa amanar da jama'ar jihar suka ba shi za ta haifar da ƙarin ci gaba da nasarori ga Jihar Ekiti da al'ummarta.
Sanarwar tazo ta hanunn
Ibrahim Kaula Mohammed
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Katsina
21 ga Yuni, 2026.
Salwa Rtv katsina..
Category
Labarai