GIDAN GWAMNATIN JIHAR KATSINA
SANARWAR MANEMA LABARAI.
Daga Salwa Rtv Katsina..
Gwamna Radda Ya Yi Ta'aziyyar Rasuwar Ɗan'uwan Wazirin Katsina.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Ida, bisa rasuwar ɗan'uwansa, Alhaji Aminu Muhammad Ida.
Marigayin ya rasu ranar Juma'a yana da shekaru 63 a duniya. Ya kasance fitaccen ɗan siyasa kuma jagora wajen ci gaban al'umma, inda ya taɓa riƙe muƙamin Mataimakin Shugaban tsohuwar Ƙaramar Hukumar Danmarna.
Gwamna Radda ya bayyana marigayin a matsayin shugaba mai kishin jama'a, mai tawali'u da sadaukar da kai wajen hidimtawa al'ummarsa. Haka kuma ya jajanta wa Alhaji Aminu Ida, Mai Bai wa Gwamna Shawara na Musamman kan Tsare-tsare, Bibiya da Tantance Ayyuka, wanda marigayin ya kasance kawunsa.
A madadin Gwamnati da al'ummar Jihar Katsina, Gwamnan ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan Ida tare da addu'ar Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya sa Aljannatul Firdaus ta zama makomarsa, Ya kuma ba iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.
Daga
Ibrahim Kaula Mohammed
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Katsina
12 ga Yuli, 2026
Wallafar Salwa Rtv Katsina..
Category
Labarai