GWAMNATIN JIHAR KATSINA TAYI JEMAMIN RASHIN SHAMSUDEEN AHMED KALA.
Gwamna Radda Ya Yi Alhinin Rasuwar Jami'in Hulɗa da Gwamnati a Abuja, Shamsudeen Ahmed.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana alhininsa kan rasuwar Alhaji Shamsudeen S. Ahmed (Kala).
Marigayin ya rasu a Abuja, inda yake aiki a matsayin Jami'in Hulɗa da Gwamnatin Jihar Katsina a Babban Birnin Tarayya. Kafin haka, ya taɓa zama Darakta Janar na Furotokol a Gwamnatin Jihar Katsina.
Gwamna Radda ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen ma'aikaci mai riƙon amana da biyayya, wanda ya yi wa jihar hidima cikin ƙwazo da tawali'u.
A madadin gwamnati da al'ummar Jihar Katsina, Gwamnan ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin, abokansa da abokan aikinsa, tare da addu'ar Allah Ya gafarta masa, Ya sanya shi a Aljannatul Firdausi, Ya kuma ba iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.
Ibrahim Kaula Mohammed
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Katsina Yabada Sanarwar.
13 ga Yuli, 2026.
..Salwa Rtv katsina muka wallafa..
Category
Labarai