Salwa RTV
Kaitsaye

ANFARA SHIRIN FAFATA GASAR NPFL NA NIGERIA 🇳🇬.

Ana Daf Da Fara Gasar Kwallon Kafa Ta NFL. 
Ƙungiyar Katsina United Ta Isa Abeokuta Domin Fara Gasar NPFL 2026/27

Yadda ‘yan wasan Æ™ungiyar Æ™wallon Æ™afa ta Katsina United suka isa garin Abeokuta domin shirye-shiryen buga wasansu na farko a gasar NPFL 2026/27, inda za su kara da Rangers International gobe, Lahadi, da Æ™arfe 4:00 na yamma.

A cikin ‘yan satin da suka gabata, Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da wasu sauye-sauye domin inganta tafiyar da Æ™ungiyar, ciki har da amfani da jirgin sama wajen tafiye-tafiye zuwa wasanni na nesa, da kuma amfani da sabuwar motar bas mai amfani da CNG wajen tafiye-tafiyen wasannin da ke kusa.

A yau, tawagar Katsina United ta samu damar yin tafiyar zuwa Abeokuta cikin jirgin kamfanin Max Air, a matsayin wani ɓangare na sabbin matakan da aka ɗauka domin sauƙaƙa wa ƙungiyar tafiye-tafiye tare da inganta shirye-shiryenta na wasanni.

Muna fatan wannan sabon tsari zai taimaka wajen samar da yanayi mai kyau ga ‘yan wasan domin mayar da hankali kan abin da ya fi muhimmanci, nasara a filin wasa.

Allah Ya basu nasara, Ya kuma dawo dasu gida lafiya.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy 
Katsina State Government 

August 29, 2026.

Post a Comment

Previous Post Next Post