Barkewar cutar mashaƙo: Gwamnatin Katsina na shirin kafa sabbin cibiyoyin killace marasa lafiya guda uku.
Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙara ƙaimi wajen dakile barkewar cutar mashaƙo wadda akafi sani da diphtheria a jihar, inda kawo yanzu aka yi wa mutane 67,670 allurar rigakafi, yayin da ake shirin kafa sabbin cibiyoyin killace marasa lafiya guda uku domin ƙarfafa kula da masu fama da cutar da hana yaɗuwarta.
Mukaddashiyar Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Lafiya Matakin Farko ta Jihar Katsina (KSPHCA), Dr. Shaima’u Kabir Abba, ta bayyana hakan a ranar Lahadi, 30 ga Agusta, 2026, yayin wani taron manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Katsina.
Ta ce ya zuwa 28 ga Agusta, 2026, an samu rahoton waɗanda ake zargin sun kamu da cutar a ƙananan hukumomi 29, inda Funtua ke da mafi yawan adadin, sai Kankia, Bakori, Katsina, Mashi da Daura.
A cewarta, an fara shirin allurar rigakafin gaggawa a ranar 25 ga Agusta, inda aka mayar da hankali kan gundumomi 15 da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar a Bakori, Charanchi, Funtua, Mashi da Kankia. An kuma tura ƙungiyoyin gaggawa, magunguna, alluran rigakafi da kayayyakin kariya daga yaɗuwar cututtuka zuwa wuraren da abin ya fi shafa.
Dr. Shaima’u ta ce ƙalubalen da ake fuskanta sun haɗa da rashin isasshen karɓar allurar rigakafin yau da kullum, jinkirin kai masu fama da alamomin cutar asibiti da kuma barazanar shigo da cutar daga ƙetare, musamman yankunan da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Ta yi kira ga iyaye, shugabannin al’umma da kafafen yaɗa labarai da su ƙarfafa gwiwar jama’a wajen yin rigakafi da kuma gaggauta zuwa asibiti idan an ga alamomin cutar, ciki har da zazzabi mai tsanani, ciwon makogaro, wahalar haɗiye abu ko numfashi, kumburin wuya, ko wani abu fari a hanci.
Hukumar ta kuma gargadi jama’a da kada su yi ƙoƙarin yin maganin cutar a gida, tana mai jaddada cewa kai mara lafiya asibiti da wuri na iya ceton rai da rage yaɗuwar cutar.
Hukumat ta gode wa Gwamnatin Jihar Katsina, abokan ci gaba, ma’aikatan lafiya da kafafen yaɗa labarai bisa goyon bayan da suke bayarwa, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da haɗa gwiwa da duk masu ruwa da tsaki har zuwa lokacin da za a shawo kan barkewar cutar.
MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government
August 31, 2026.
Wallafar Salwa Rtv katsina
Category
labarai