Gamayyar ƙungiyoyin matasa masu goyon bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu sun yi Allah wadai tare da yin tir ga al'ummar da suka yi wa Dr. Abu Ammar kalaman ɓatanci.
A wata sanarwa da Sakataren Tsare-tsare na Gamayyar Ƙungiyoyin Matasa Masu Goyon Bayan Tinubu, Aminu Tanimu Turaki, ya sanya wa hannu a ranar Litinin, 13 ga watan Yuli, 2026, ƙungiyar ta yi tir tare da yin Allah wadai da kalaman ɓatanci da wasu mutane suka yi wa Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Dr. Abu Ammar, sakamakon wani suna da yakira Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu dashi.
Sanarwar ta bayyana cewa tun da farko akwai wasu mutane da ke jiran samun wata dama domin su riƙa yin ɓatanci ko kuma su ɓata wa Shugaban Hukumar Hisbah suna, saboda ayyukan gyaran tarbiyya da hukumar ke gudanarwa. A cewar sanarwar, sun yi amfani da wannan batu ne a matsayin hujjar kai masa hari.
Sanarwar ta ƙara da cewa a Najeriya kowane ɗan ƙasa yana da 'yancin faɗin ra'ayinsa kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin ƙasa ya tanada. Saboda haka, kamar yadda kowane ɗan Najeriya ke da wannan hakki, haka ma Dr. Abu Ammar yana da cikakken 'yancin bayyana ra'ayinsa.
Ta kuma ce, kasancewar Jam'iyyar APC ce ta naɗa Dr. Abu Ammar a matsayin Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, babu laifi idan ya yi magana kan harkokin jam'iyyar ko ya bayyana ra'ayinsa mai kyau game da wani shugabanta.
A ƙarshe, ƙungiyar ta ja hankalin tare da gargaɗin masu ci gaba da yin kalaman ɓatanci ga Dr. Abu Ammar da su ji tsoron Allah su daina. Ta kuma bayyana cewa kasancewar su masu laifi agare shi, ya dace su nemi afuwa daga gare shi.