Salwa RTV
Kaitsaye

KASEDA na da burin zama abin koyi a Afirka wajen bunƙasa kasuwanci.. Jihar Katsina


DAGA GIDAN GWAMNATIN JIHAR KATSINA
TAKAITACCEN SANARWAR MANEMA LABARAI. 

Ma Aikatar KASEDA na da burin zama abin koyi a Afirka wajen bunƙasa kasuwanci. 

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa gwamnatin jihar na da burin ganin Hukumar Bunƙasa Kasuwanci ta Jihar Katsina (KASEDA) ta zama abin koyi a Najeriya da ma nahiyar Afirka  wajen haɓaka ƙananan da matsakaitan sana'o'i (MSMEs).

Mataimakin Gwamna Jihar, Alhaji Faruk Lawal Jobe, wanda shine ya wakilci Gwamnan a taron Kwamitin Gudanarwar ta KASEDA da aka gudanar a Jihar Neja, ya ce manufar gwamnati ita ce gina hukuma mai ƙarfi wadda za ta inganta kasuwanci, samar da ayyukan yi, rage talauci da bunƙasa tattalin arziki.

Ya ce Katsina ta riga ta samu yabo a matakin ƙasa bayan KASEDA ta lashe lambar Mafi Kyawun Hukumar Bunƙasa sana'o'i MSMEs ta Jiha a Najeriya, tare da samun fitaccen ɗan kasuwa daga jihar da ya lashe babbar kyauta ta MSMEs ta ƙasa.

Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin shirin KASEDA Road Corridor Enterprise Infrastructure Programme, wanda ya tantance sana'o'in da ke kan manyan hanyoyi a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar, domin sauƙaƙa tallafi da samun jari domin faɗaɗa kasuwanni da inganta rayuwar al'umma.

A nasa jawabin, Darakta Janar na KASEDA, Dr. Babangida Kabir Ruma, ya ce hukumar za ta mayar da hankali kan samar da sakamako mai amfani ga 'yan kasuwa ta hanyar inganta samun kuɗaɗen jari, kasuwanni, fasaha, hanyoyin zamani da kuma haɗin gwiwa.

Shi kuma Babban Mai Gabatar da Taro kuma Shugaban CRC Credit Bureau, Ahmed Tunde Popoola, ya bayyana cewa ƙananan da matsakaitan sana'o'i su ne ginshiƙin sauya tattalin arziki, yana mai kira ga KASEDA da ta rungumi tsarin zamani da ya haɗa da amfani da fasahar zamani, rajistar MSMEs ta dijital, bayanai masu inganci da haɗa 'yan kasuwar Katsina da kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje.

Ibrahim Kaula Mohammed
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Katsina
11 ga Yuli, 2026
            Salwa Rtv katsina.. 

Post a Comment

Previous Post Next Post