Gomnan jihar katsina malam Dikko Radda, da tsohon gomna Shema da kansu sukaje majalisar wakilai Domin karɓar Salisu Yusuf Majigiri, Da Abdullahi Dabai da Muhammad Iliyasu dukkansu yan majalisar wakilai ne na PDP Jam'Iyar adawa daga jihar Katsina da suka sauya sheka zuwa APC Jam'Iya Mai Mulki gaba ɗayansu
Ƴan majalisun da suka sauya sheka da suka hada da Hon Abdullahi Balarabe Dabai da ya ci zabe a PDP, sai kuma Yusuf Majigiri na mazabar Mashi/Dutsi da kuma Muhammad Iliyasu na mazabar Batsari/Safana/Danmusa
A ɗalilan da suka bayar sun ce PDP fitintinun cikinsu sun yi yawa, kuma sun bayyana gamsuwarsu da yadda gwamna Dikko Radda ke tafiyar da mulki a jihar Katsina
Daga ciki ƴan majalisar da suka halarci wannan zama da yi wa gwamna Dikko Radda maraba lale a zauren Majalisar har da dan majalisar Kankara/Faskari/Sabuwa Hon Shehu Dalhatu Tafoki da Hon.Sada Soli Jibiya/Kaita sai Hon.AID Mani Bindawa da dai Sauransu.
Salwa Rtv online media services
Category
Labarai