Salwa RTV
Kaitsaye

Gomna Dikko Radda ya sake bode kasuwar shanu ta sheme bayan tsawon lokaci tana rufe.

Labari Da Duminsa: Dikko Radda Ya Buɗe Kasuwar Shanu Ta Sheme, Ta Fara Ci Gadan-gadan A Yau Jumu’a

A safiyar yau Jumu’a ne aka dawo da cin kasuwar shanu da ke garin Sheme, a karamar hukumar Faskari, Jihar Katsina, wadda ake gudanarwa a duk ranar Jumu’a.

Kasuwar ta kasance a rufe na tsawon shekara ɗaya da rabi, sakamakon wasu matakan tsaro da gwamnatin jihar ta ɗauka.

Sakataren kwamitin buɗe kasuwar, Alhaji Sa’idu Ya’u, wanda kuma shi ne Rabanu Ofisa na karamar hukumar Faskari, ya shaida wa majiyar Funtua Post Katsina Daily News cewa an buɗe kasuwar yau cikin nasara.

Ya bayyana cewa an kafa kwamitin kula da gudanar da kasuwar karkashin jagorancin Shugaban jami’an tsaron C-Watch, inda shi (Alh. Sa’idu Ya’u) ke matsayin sakatare.

Ya ƙara da cewa sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Hakimi, Sarkin Kasuwa, Sarkin Shanu, Sarkin Turaku, da Zanguna, tare da wakilan addinai: Malam Yaro (Izala) da Malam Shitu Sani (Ɗarika).

Post a Comment

Previous Post Next Post