AL'ƘALAMINA BINDIGATA.
"Tsokaci akan makomar aikin Jarida a Jahar Katsina"
DAN JARIDA A JIHAR KATSINA;
DAMBE KO KOKOWA.. ABOKIN AIKI KO MABARACI??
______________________
Duk da irin mahimmancin da Aikin Jarida yake da shi acikin rayuwar al'umma,musamman a mulkin Demokaradiya. Da duk irin sadaukarwa, jajirtacewa, tare da ƙoƙarin da Ɗan Jarida ke yi acikin rayuwar al'umma, tare da bawa gwamnati gaggarumar gudunmuwarsa, wajen yaɗa tare da wallafa aikace-aikacen ta, manufofinta, tare da tallata ƙudirinta na Alkhairi ga Al'umma!
Amma kash!
A jaharmu ta katsina, Aikin Jarida, tare da shi kanshi Ɗan Jaridar na fama da tsangwama, hantara tare da wonfitarwa! A katsina Ɗan Jarida ya zama tamkar MABARACI, Mamugunci, abin ƙyama duk da irin mahimmancin da yake da shi, da kuma irin gudunmuwar da yake bayarwa acikin al'umma dama Gwamnatin kanta gaba ɗaya!
Assallamu Alaikum: Zuwa ga Shugabani da mahukunta.
Zuwa ga Gwamnati
Zuwa ga shuwagabannin Ƙungiyoyin Jarida
Zuwa ga shugabanin Online Media (New Media)
Zuwa ga Shuwagabannin Tsaro.
Sunana Rabiu M. Yro Salwa Radio And Television (Online Media Serrvices) Ɗan ƙaramin cikinku kuma mai koyon aikin Jarida, don haka Idan anga na yi kuskure to dan Allah ayafeni domin hakanma na daya daga cikin koyo .
Tare da girmamawa agareku baki daya.
Akwai abubuwa da dama da suke cimin tuwo a kwarya wanda sau dayawa nake tambayar kaina anya kuwa muna yin Aikin nan daidai kuwa?, ko kuma dai an daina bukatar aikin jaridar ne a jahar Katsina!? Domin Idan na tsaya na kalli yadda ake martaba magabatanmu tare da girmamasu, kaina ya kan kulle, in rasa daga ina tamu matsalar ta ke!? Miyasa yanzun muka rasa wannan ƙiimar da Darajar?
A zahirin gaskiya ana wulaƙanta Ɗan Jarida ana cin mutuncinsa ana cin zarafinsa a wannan Gwmnatin kuma kowa yana gani a gaban Idon kowa hakan take faruwa amma kuma kowa yaja baki yayi shiru.. Shin tsoro ne ko kwadayi!?
Daga 29/5/2023 Zuwa wannan rana ta 29/5/2025
Idan muka auna zamu iya cewa ansamu shekara 2 cif-cif Amma har yau ba'adaina hantarar Ƴan Jarida ba. Idan daga farkon mulki ance ba'agama sanin mu ba to har yau ba'asanmu ba kenan!? (Abin takaicin, Babu babba ba yaro, kowa wulaƙantawa su ke!)
Idan aka Lissafa yawan tarukan da wannan gwamnatin ta yi a tsawon shekara 2 muna Iya cewa babu wanda ba'aci mutuncin dan Jarida ba. Amma fa wannan hasashena ne bance lallai sai ya zama dai dai da naka ba yallabai. Bari mudan tsakoro kadan daga ciki;
Akwai taruka kamar haka
1.Ranar da aka rantsar da Kwamishinoni,,wanda duk yaje na san ya ganema Idonsa yadda akayi da ƴan Jarida.
2.Rantsar da Ciyamomi nan ma wani Bawan Allah har saida aka nemi fasa masa Ido agurin.
3.Zuwan Ɗan Shugaban Kasa watau Sheyi Tunibu nan ma har sai da wata mace Jami'ar Farin Kaya ta Kwace wayar wani dan Jarida.
4.Zuwan Shugaban kasa nan akayita kowa ya gani domin Kashi 9 da rabi cikin goma basu Iya shiga gurinda aka ƙaddamar da wannan aikin ba!
Wa'annan kaɗan ne na dan tsakuro daga cikin dubbai. Don haka mu ke roƙo shuwagabaninmu na bangaren aikin Jarida da Iyayen gidanmu da mu ke koyon wannan aiki agaresu da suwa Allah sudubi wannan yanayi da muke ciki su nema mana mafita. Domin Idan fa aka cigaba da tafiya Irin haka to darajar aikin zata tabu.
Ko ba komai amutuntaka ko ba'a baka komai ba ai kaji sanyi sanyi aranka amma yadda ake mana tukin gangancinnan wlh yayi yawa Jami'in tsaro yayi maka tsawa wani ma ya tunkuɗeka da kai da kayan aikink, shin basu gudun wani ya karya kafa ko hannu ko Kuma ayi hasarar kayan aikin?
Kai da baka da albashi ba ka da wani tsayayyen alawus da aka ware don kai kuma ka dage ka na ta yaɗa ayyukan gwamnati kyauta ruwan Allah amma kuma mai albashi ya na neman nakasaka kuma ka ja baki kayi shiru haba dan Uwa!
Hausawa na cewa; Da rashin magana karen kurma ya bace! Idan Mu kayi duba da wasu Jihohin yadda ake karrama masu aiki irin namu sai ku ha mamaki kodayake mu yanzun mu ke koyon aikin amma dai dan girman Allah ku nema mana ƳANCI agurin wannan gwamnati tunda dai bamu da yadda za mu yi, a nan Allah yayi abincin
Amma fa ni Rabiu M. Yaro zan iya ajiye wannan aikin a wannan tafiyar matsawar aka cigaba da cin mutuncina domin ni dai Ina son wannan tafiya kuma ina yi mata kyakyawar fata.
Allah yasa mudace duniya da lahira!
Category
Labarai