Bikin ranar yara ta duniya
Yau dai Allah Ya cika ma yayan gwamna Dikko Radda gurinsu na saka kayan yan sanda
Za a iya tuna cewa a kwanakin baya yaran na gwamna sun ga wani yaro dan wani dan sanda sanye da kayan yan sanda suka roki baban nasu, inda a cikin raha ya ce masu "to ai su babansu dan sanda ne"
A wajen bikin ranar yara ta Duniya da aka yi yau a Katsina an hango gwamnan yau tare da yaran nasa sanye da kakin yan sanda, kuma ya yi masu kyau gwanin ban sha'awa
Salwa radio and television online media services.
Category
Labarai