Tsohon Sanata Na’Allah Ya Koka Da Wahala, Ya Ce Da Yawa Ba Su Iya Biyan Kudaden Makarantar Yara Bayan Sun Bar Ofis
Tsohon Sanata Bala Ibn Na’Allah, ya ce wasu ‘yan majalisar a Najeriya sun shiga cikin mawuyacin hali bayan sun bar Majalisar Dokoki ta kasa, ta yadda suke ta faman biyan kudin makarantar ‘ya’yansu.
Da yake magana a cikin shirin mintuna 30 na Trust Television, tsohon dan majalisar dattawan Kebbi ta Kudu ya kalubalanci akidar da ake ta yadawa cewa aikin gwamnati shine tabbacin hanyar samun arziki.
#DailyTrueHausa
Category
Labarai