Salwa RTV
Kaitsaye

Kiwon Lafiya Kyauta Yana cigaba da Samun Tagwa mashi a Jihar Katsina..


DAGA GIDAN GWAMNATIN JIHAR KATSINA. 
SANARWAR MANEMA LABARAI. 

Kiwon Lafiya Kyauta Na Ci Gaba da Zama Fifikonmu Inji Gwamna Radda. 

Gwamnatin Katsina ta fara rabon magunguna da kayan aikin asibiti na kyauta daga Project CURE. 

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ƙaddamar da rabon magunguna da kayan aikin asibiti na kyauta da ƙungiyar Project CURE ta bayar domin amfanin asibitocin jihar.

A wajen ƙaddamarwar, Gwamnan ya ce wannan tallafi wani muhimmin mataki ne na ƙara inganta harkokin lafiya da kuma tabbatar da cewa al'ummar jihar suna samun ingantaccen kulawa ba tare da la'akari da halin kuɗinsu ba.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ƙara kasafin shirin Free Medicare da kashi 207%, lamarin da ya ba da damar faɗaɗa shirin zuwa ƙarin mata masu juna biyu, yara ƙasa da shekara biyar, masu fama da zazzabin cizon sauro, da kuma masu buƙatar maganin cizon maciji da na cutar rabies kyauta.

Gwamna Radda ya kuma ce ana ci gaba da bunƙasa Hukumar Samar da Magunguna ta Jihar ta hanyar kammala masana'antar samar da magunguna, ƙara motocin jigilar magunguna da kuma faɗaɗa shirin Drug Revolving Fund zuwa cibiyoyin lafiya na matakin farko 361 da aka inganta.

A nata jawabin, Babbar Sakatariyar Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Asibiti ta Jihar Katsina, Pharmacist Fatima Shuaibu, ta bayyana cewa tun bayan fara gyaran tsarin lafiya na gwamnatin Radda, adadin ma'aikatan hukumar ya ninka daga 34 zuwa 70, yayin da Drug Revolving Fund ya haɓaka da kashi 400%, sannan yawan cibiyoyin da ake kai wa magunguna ya ƙaru daga 50 zuwa kusan 200.

Ta ƙara da cewa hukumar ta fara amfani da tsarin dijital wajen sarrafa odar magunguna, tare da kusan kammala masana'antar samar da magunguna da za ta fara samar da nau'ikan magunguna shida kafin ƙarshen shekarar nan.

Ta yabawa Gwamna Radda bisa ci gaba da ba hukumar cikakken goyon baya, tana mai cewa hakan ya inganta samar da magunguna da ayyukan kiwon lafiya ga dubban al'ummar jihar.

Ibrahim Kaula Mohammed
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Katsina Ya Rubuta. 
16 ga Yuli, 2026.
         Wallafar Salwa Rtv Katsina.. 

Post a Comment

Previous Post Next Post