Salwa RTV
Kaitsaye

MULEQA KANNYWOOD Nis

MULEQA KANNYWOOD 

ABINDA ALI NUHU YA FADA A KAN MATARSA CIKIN JAMAA….

Bana cin abinci a waje…… Ali Nuhu

Sama da shekaru 20 da aurena da Maimuna (matata) bantaba cin abinci a waje ba, muddin ina kano, duk nisan wajen zata kawo abincina har wurin dan naci.

Wannan ba Komai bane face kauna da muka gina tsakaninmu tun muna saurayi da Budurwa, ya kara da cewa ita mace: muddin zaka tattalata ka bata kulawa, ko shakka babu zaka samu kulawa fiye da baka zato daga gunta.

Ko dayake yace shi malamine a fagen soyayya shiyasa, soyayyar dayake nunawa a fina-finansa yake nunawa a zahiri ga iyalinsa.

Ya kara da cewa tsahon shekarun da suka dauka babu wanda ya tabajin kansu shi da matarsa ba, saboda yana kokarin kiyaye duk abinda zai kawo matsala cikin iyalinsa.

Zuwa dai yanzu, Alinuhu yana da yaya biyu Fatima wacce ta kammala karatunta daga jami’ar Skyline dake kano sai Ahmad dake cigaba da karatu haryanzu.

Daga Abdussamad Ishaq
     SALWA RADIO AND TELEVISION ONLINE MEDIA SERVICES KATSINA.

Post a Comment

Previous Post Next Post