Mutane uku da suka rasu a wata kasa kuma ba yan kasar Saudi arebiya ba aka yi jana’izarsu a Masallacin Harami Madina.
Tarihi ya nuna cewar waɗannan mutanen su kaɗai ne suka samu wannan dacen:
1. Muhammad Al-Badr – Shi ne Sarki na ƙarshe a ƙasar Yemen kafin juyin mulki ya kifar da mulkinsa. Ya rasu ne a birnin London a shekarar 1996.
2. Zine El Abidine Ben Ali – Tsohon shugaban ƙasar Tunisia wanda ya mulki ƙasar na tsawon lokaci kafin juyin juya hali. Ya rasu ne a birnin Jeddah, Saudiya, a shekarar 2019.
3. Alhaji Aminu Alhassan Dantata – Fitaccen ɗan kasuwa daga Kano, Najeriya. Ya rasu ne a birnin Abu Dhabi, Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), ranar Asabar 28 ga Yuli, 2025.
Dukkan waɗannan fitattun mutane, iyalan su sun nemi izinin gwamnatin Saudiyya domin gudanar da sallar jana’iza a cikin Masallacin Harami da ke birnin Madina mai alfarma — buƙatar da ba kasafai akan amince da ita a kowane lokaci ba.
Kamar yadda Jaridar Zinariya ta wallafa
Allah Ya jaddada masu rahama.
Follow 👉 Salwa radio and television online media services Katsina
Category
Ketare