Salwa RTV
Kaitsaye

Ƙungiyar Kanikawa (NATA) Ta Goyi Bayan Shugaba Tinubu da Gwamna Radda a Zaɓen 2027

Ƙungiyar Kanikawa (NATA) Ta Goyi Bayan Shugaba Tinubu da Gwamna Radda a Zaɓen 2027

Ƙungiyar ƙwararrun masu gyaran motoci ta ƙasa, National Automobile Technicians Association (NATA), ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, a zaɓen 2027, tana mai bayyana cewa hakan ya samo asali ne daga jajircewar gwamnatocin biyu wajen inganta rayuwar matasa, bunƙasa sana’o’i, da tallafa wa masu sana’o’in hannu.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban NATA, Alhaji Abbati, ya ce matakin ƙungiyar na nuna irin amincewar da mambobinta ke da ita ga manufofi da shirye-shiryen gwamnatocin Shugaba Tinubu da Gwamna Radda. Ya bayyana cewa mambobin NATA a faɗin ƙasar za su gudanar da gangamin wayar da kai da kuma neman goyon baya domin sake zaɓen shugabannin biyu a 2027.

A nasa jawabin, Darakta-Janar na Hukumar Bunƙasa Harkokin Kasuwanci ta Jihar Katsina (KASEDA), Dr. Babangida Ruma, ya yaba wa NATA kan wannan matsaya, tare da jaddada cewa gwamnatin Jihar Katsina za ta ci gaba da tallafa wa masu sana’o’in hannu, ƙwararrun masu gyaran motoci da ƙananan ’yan kasuwa ta hanyar shirye-shiryen ƙarfafa gwiwa, koyar da sana’o’i da bunƙasa harkokin kasuwanci.

Shi ma Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Dr. Bishir Gambo Saulawa, ya bayyana wannan goyon bayan a matsayin wata babbar shaida ta amincewa da manufofi da ayyukan gwamnatocin APC. Ya buƙaci mambobin ƙungiyar da su ci gaba da wayar da kan jama’a da ƙara ƙaimi wajen tattaro mutane a matakin ƙasa domin samun nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027.

Da yake jawabi, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya nuna godiya ga NATA bisa wannan goyon baya, tare da sake tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ƙarfafa matasa, bunƙasa koyar da sana’o’in hannu da fasaha, da kuma samar da yanayin da zai ba masu sana’o’in hannu damar haɓaka harkokinsu.

A madadin masu koyon sana’a na ƙungiyar, daya daga cikinsu ya bayyana jin daɗinsu kan shirye-shiryen ƙarfafa gwiwa da suka amfana da su, tare da tabbatar da cewa su ma za su ci gaba da mara wa Shugaba Tinubu da Gwamna Radda baya, tare da taimakawa wajen tattara ƙuri’u a matakin ƙasa domin samun nasarar su a zaɓen 2027.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy 
Katsina State Government 

August 19, 2026.

Post a Comment

Previous Post Next Post