Gwamna Radda Ya Yi Ta’aziyya Ga Shugaban Shirin CDP Kan Rasuwar Abokiyar Zaman Mahaifiyarsa.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya mika sakon ta’aziyya ga Shugaba Mai Gudanar da Shirin Raya Al’umma (CDP), Assoc. Prof. Kamaladden Kabir, bisa rasuwar Abokiyar Zaman Mahaifiyarsa, Hajiya Sa’adatu Kabir, mai shekaru 75.
Hajiya Sa’adatu ta rasu a ranar Talata bayan Fama da doguwar rashin lafiya, Sanan anrinaga anyi Zana'idarta kamar Yadda tsarin addinin Musulunci Ya Tanada. Ta Rasu
Ta bar ’ya’ya 10.
Gwamna Radda ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi,ga Iyalai dama Yan'uwa da abokanan arziki dama Jihar Baki da ya a matsayinta na Uwa, yana mai cewa ta kasance uwa mai kula da Rayuwar Iyalanta, sanan
Ya bukaci iyalan marigayiyar su yi hakuri tare da mika al’amarinsu ga Allah.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah Yajikanta ya gafarta mata kura-kuranta, Ya kuma ba iyalanta hakuri da juriyar wannan rashi.
Ibrahim Kaula Mohammed
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Katsina
18 ga Agusta, 2026
Wallafar Salwa Rtv.
Category
Labarai