Salwa RTV
Kaitsaye

Zaman gidan yari na har abada ga duk macen da takara nuna tsiraicinta a social media

Daga Yau dokar Zaman gidan yari Na dindindin ta Fara Aiki a ƙasar Bulkina Faso ga Mata Masu Nuna Bidiyon tsaraici a kafafan Sada Zumunta a ƙasar Bulkina Faso, inji Ibrahim Traore

Shugaban Kasar Burkina Faso Ibrahim Traore Yace daga Yau doka ta fara Aiki, inda Ya saka dokar biyan tarar miliyan biyu da zaman gidan yari Na dindindin ga duk macen da ta bayyana tsiraicinta a kafafen sadarwa na zamani.

Yace Hakan Babbar Illaci Ga Alumma Domin Yana Janyo Su Shagaltu Da Abubuwan Sabon Allah Ya Kuma Rage Masu Kuzarin Kishin Addini Da Kasar Su.

Daga ƙarshe yasa An Rufe Dukkanin Shafukan Yada Badala A Yanar Gizo A Kasar Burkina Faso Kamar Yanda Shugaban Kasar su ya Bukata.

Bayan Dakatar Da Duk Wasu Shirye Shiryen Fina finai Masu Nuna Tsaraici A Kasar Ta Burkina Faso, Ibrahim Traore Ya Bukaci A Rufe Dukkanin Shafukan Yada Badala A Yanar Gizo A Kasar Tashi Ta Burkina Faso.

Ya Ce Africa An San Mu da Martaba Al'adunmu Da Addinimu Saboda Haka Ni Ba Na Goyon Bayan Komawa Baya Irinta Turawa Saboda Haka Ya Bayyana Cewa Dukkanin Yan Film Su Shiga Taitayinsu Su Kame Jikinsu Bisa Tsarin Addini Da Al'adu.

Post a Comment

Previous Post Next Post