DA DUMI-DUMI:" EFCC ta kama Gudaje Kazaure bisa zargin karbar Naira milyan N70 daga hannun tsohon shugaban CBN Emiefele
Daga Salwa Rtv
Hukumar EFCC ta kama tsohon dan majalisar Jigawa Muhammad Gudaje Kazaure bisa zargin karbar Naira milyan N70 daga hannun tsohon shugaban babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emiefele
Bayanai sun nuna dan majalisar ya amshi kyautar Naira milyan 20 daga Emiefele ta hannun wani Mista Eric a matsayin kudin ragon sallah ko Goron Sallah
Sannan a wani lokaci kuma ya sake karbar Nairn milyan N50 a matsayin gudunmawa bisa iftila'in gobara da ta afkawa wani sashi na gidansa.
Taskar Labarai ta ruwaito a watan Disamba 2022 Mista Kazaure ya zargi Shugaban CBN Emiefele da karkatar da akalla Naira Triliyan N89.1 kudin "Stamp Duty" da ake caza a bankuna
(Majiya)~Taskar Labarai
Salwa Radio and television
Category
Labarai