Ka Cika Alkawuran da Kayi wa Mutanen Dandume a Yakin Neman Zaben da ya Gabata” — Magajin Dandume Ya Yabawa Gwamna Radda
Katukan Katsina kuma Hakimin Dandume, Alhaji Jafar Ibrahim, wanda ya samu wakilcin Magajin Garin Dandume, ya yaba wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, bisa cika alkawuran da ya ɗauka wa al’ummar Ƙaramar Hukumar Dandume a lokacin yaƙin neman zaɓen shekarar 2023.
Hakimin ya bayyana hakan ne a lokacin da Gwamna Radda ya kai masa ziyarar ban-girma a fadarsa, a rana ta uku ta gangamin yakin Neman Zaɓen Tinubu/Dikko 2027 da ake gudanarwa a faɗin jihar inda ya gana da sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki na Karamar Hukumar Dandume.
“Na karɓe ku a nan a lokacin yaƙin neman zaɓen shekarar 2023, kuma zan iya tabbatar muku da cewa kun cika dukkan alkawuran da kuka ɗauka wa mutunenmu,” in ji Magajin Dandume.
Ya bayyana jin daɗinsa musamman kan ɗaga matsayin Babban Cibiyar Kiwon Lafiya ta Dandume (CHC) zuwa Babban Asibiti, samar da kayan aikin noma, gyare-gyaren da aka yi wa sarakunan gargajiya da malaman addini, shirye-shiryen bayar da tallafin karatu, Shirin Bunƙasa Al’umma (CDP), da sauran ayyukan raya fannonin ilimi, tsaro, noma da kiwon lafiya.
A nasa jawabin, Gwamna Radda ya bayyana cewa ziyartar sarakunan gargajiya al’ada ce da tawagar yaƙin neman zaɓen ke bi a dukkan wuraren da ta ziyarta. Ya kuma yi tsokaci kan sauye-sauye da gwamnatinsa ta kawo a hukumomin sarakunan gargajiya da na addini, shirye-shiryen bunƙasa al’umma da kuma tallafin da ake bai wa harkar noma, musamman noman rani.
Gwamnan ya sake jaddada cewa ɗaga matsayin Babban Cibiyar Kiwon Lafiya ta Dandume zuwa Babban Asibiti na daga cikin ƙudurin gwamnatinsa na cika alkawuran da ta ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023. Haka kuma, ya sanar da amincewa da shirin zamanantar da Kasuwar Dandume.
Haka kuma, Gwamnan ya yi tsokaci kan ci gaban da aka samu a fannin tsaro, tare da bayyana muhimmancinsa wajen bunƙasa harkokin noma da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma a yankin. Ya kuma bayyana shirye-shiryen da gwamnatinsa ke aiwatarwa domin ƙarfafa al’umma ta hanyar Shirin Cigaban Al’umma (CDP).
Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da kasancewa cikin alaka da shugabanninsu, tare da bayyana goyon bayansu ga jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027.
Bayan ziyarar ta fadar hakimin, Gwamna Radda ya kuma gana da manyan masu ruwa da tsaki na Ƙaramar Hukumar Dandume, inda suka tattauna muhimman batutuwan siyasa, ci gaba da hanyoyin bunƙasa ƙaramar hukumar.
Manyan jami’an da suka halarci tarukan sun haɗa da Mataimakin Gwamna, Malam Faruk Lawal Jobe; Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe, Arc. Ahmed Musa Dangiwa; Mataimakin Shugaban Kwamitin, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa; Sakataren Kwamitin, Abdullahi Aliyu Turaji; da Shugaban Ma’aikatan Gwamna, Hon. Abdulakadir Mamman Nasir, tare da sauran jami’an gwamnati, shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki.
MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government
October 30, 2026.
#Tinubu2027
#Radda2027
#KatsinaDecides
#BuildingYourFuture