Gwamna Radda Ya Yi Jimami tare da Ta'aziyyar Rasuwar Alhaji Abu Danmalam Karofi ADK Raya Karkara.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya bayyana alhininsa bisa rasuwar tsohon ma’aikacin gwamnati kuma tsohon Sakatare na Din-din-din, Alhaji Abu Danmalam Karofi, wanda aka fi sani da ADK, ko “Raya Karkaran Katsina.”
Marigayin ya rasu a yau bayan gajeriyar rashin lafiya, yana da kimanin shekaru 35 na hidimar gwamnati a tsohuwar Jihar Kaduna da Jihar Katsina.
Gwamna Radda ya bayyana shi a matsayin gogaggen ma’aikacin gwamnati, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban jihar, musamman harkokin ƙananan hukumomi.
Alhaji Abu Danmalam Karofi ya taɓa zama Sakatare na Din-din-din da Mai Ba Gwamna Shawara kan Ƙananan Hukumomi da Masarautu a lokacin mulkin Marigayi Umaru Musa Yar’adua.
Gwamna Radda ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da sauran al’ummar Katsina, tare da roƙon Allah Ya gafarta masa, Ya jiƙansa, Ya kuma sanya Aljannatul Firdaus ce makomarsa.
Wallafar Salwa Rtv Katsina.
Category
Labarai