Salwa RTV
Kaitsaye

Obama Yayi kakkausar Suka akan Shugaba Trump

Tsohon shugaban ƙasar Amurka, Barack Obama, ya yi suka kan matakin da shugaban Amurka na yanzu, Donald Trump, ke ɗauka game da rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran.
A cikin wata sanarwa da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, Obama ya ce Trump na gab da fahimtar dalilin da ya sa shugabannin Amurka guda bakwai tun daga shekarar 1979 suka guji shiga yaƙi kai tsaye da Iran. Ya bayyana cewa wannan yaƙi na iya jefa Amurka cikin wani rikici mai girma wanda yawancin Amurkawa ba sa so.
Obama ya kuma yi kira ga al’ummar Iran da su fahimci cewa ba dukkan Amurkawa ne ke goyon bayan wannan rikici ba, yana mai cewa rikicin da ake fuskanta a yanzu ya samo asali ne daga manufofin Trump, ba daga ra’ayin al’ummar Amurka gaba ɗaya ba.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin siyasa da na soja tsakanin Amurka da Iran ya ci gaba da ɗaukar hankali a duniya, yayin da masana ke gargadin cewa duk wani sabon mataki na iya ƙara tsananta rikicin a yankin Gabas ta Tsakiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post