Ibrahim Badamasi Babangida Yayi maganar da tasaka wasu manyan Arewa kuka da hawaye ganin yadda yankin yake neman durkushewa...domin Idan akatafi ahaka to tabas za'awayi gari anshafe wannan yanki namu na Arewa..
Ga bayanin akanmale
Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Gen, Ibrahim Badamasi Babangida ya nemi shugabannin Arewa da su ceto yankin daga durƙushewa, a wani jawabin daya gudanar da Asubahin yau, Gen, Babangida yace "Kunga dai duk manyan dattawan yankin suna ta faɗuwa suna mutuwa tun daga manyan malaman addinin siyasa da dai sauran su, nima kaina ina ji a jikina daƙyar idan wannan wannan shekarar zata fita ban koma ga Allah ba, fatanmu dai shine cikawa da imani".
"Saboda haka ina kira ga shugabannin wannan yanki namu, na arewa, mu dai lokacin da muke da dama mun yi iya abinda za mu iya, da ace na bar babban birnin tarayya a jihar Legas, ban dawo da shi yankina na arewa ba to da yanzu ba'a ma san inda arewar take ba, Alhamdu Lillahi mun yi iya abinda zamu iya yanzu mu tamu tazo ƙarshe don Allah shugabannin arewa ku haɗa kan ku ku ƙwaci yankin nan namu domin bamu da kamar sa".
In ji shi kamar yadda ya bayyana a jawabin nasa.
Copied
Category
Labarai