Salwa RTV
Kaitsaye

Wani Kare yasamu gata bayan mutuwarsa anyimasa zana'iza domin yimasa kabari.

Kare Wizzy Ya Rasu, Al’umma Sun Yi Masa Jana’iza a Mahuta

A safiyar Talata da misalin ƙarfe 8:00 na safe, al’ummar garin Mahuta sun gudanar da jana’iza da binne wani kare mai suna Wizzy, mallakin marigayi Abdullahi ɗan Alhaji (wanda aka fi sani da Cuwa Cuwa).

Bayan kammala binne wizzy jama’ar da suka halarta sun yi addu’o’i na neman rahama ga mamallakin karen marigayi Abdullahi.
Wizzy yadade ana fafatawa dashi a fagen daga domin bada kariya ga al'ummar wannan gari,

Rahotanni sun nuna cewa akalla mutane 50 ne suka halarci wannan taron, ciki har da shugaban ‘yan Vigilante na garin Mahuta, Ado Usman Mahuta.

Al’umma sun bayyana alhinin su tare da addu’ar Allah ya musanya musu da mafi alkhairi.
    Salwa radio and television online media services Katsina.

Post a Comment

Previous Post Next Post