Salwa RTV
Kaitsaye

Duk Dalibin da aka yaye daga makarantar koyar da noma da kiyo zai karbi 1m domin fara sana'a. Inji Gomnatin Jihar Katsina.

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayyana cewa kowane dalibi da ya kammala makarantar Songhai Comprehensive Center dake Maƙera, Dutsinma, zai samu kudi Naira miliyan ɗaya (N1m) a matsayin jari don fara sana'ar noma da kiwo.

​Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye ɗalibai na farko da suka fito daga makarantar. A yayin wannan shiri, an yaye ɗalibai guda 102, inda aka zaɓi mutane uku-uku daga kowace ƙaramar hukuma cikin ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina.

​Bayan sun shafe tsawon watanni suna samun horo a fannoni daban-daban na noma da kiwo, ɗaliban sun kammala karatunsu. An yaye su don su koma garuruwansu su yi amfani da hikimomi da fasahohin da suka koya don amfanar da al'ummominsu.

​A nasa jawabin, Kwamishinan Noma da Raya Karkara, Hon. Bakori, ya yi godiya ga Gwamnan bisa wannan shiri mai albarka da kuma irin goyon baya da ya bayar don ganin shirin ya tabbata. Ya kuma bayyana cewa an horar da ɗaliban ne yadda za su dogara da kansu ta hanyar ilimin da aka ba su da kuma jarin da za a basu, har ma su dauki wasu aiki.

​A nasa jawabin, Gwamna Dikko Radda, Ph.D, CON, ya taya ɗaliban da aka yaye murna, sannan ya gode wa malamai da ma'aikatar noma bisa jagoranci da kuma jajircewarsu wajen ganin an cimma wannan buri. Gwamnan ya sanar da Naira miliyan ɗaya a matsayin jarin fara kasuwanci ga kowane ɗalibi don ya dogara da kansa. Gwamnan ya ƙara da cewa irin waɗannan shirye-shiryen suna cikin manyan tsare-tsare na gwamnatinsa na bunƙasa aikin gona, samar da guraben aikin yi, da kuma farfado da tattalin arzikin jihar Katsina.

​Gwamnan ya yi kira ga ɗaliban da su mai da hankali kuma su yi amfani da jarin da suka samu yadda ya kamata don ci gaba da dogara da kansu. Ya kuma bayyana cewa duk wanda ya nuna kwazo kuma ya bunƙasa kasuwancinsa, hukumar bunƙasa kasuwanci ta jihar, wato KASEDA, a shirye take ta tallafa masa ta hanyar ba shi rance ba tare da ruwa ba, don ci gaba da bunƙasa kasuwancinsa.

​Manyan baki da suka halarci taron sun haɗa da Mataimakin Gwamna. Malam Faruk Jobe, wakilin Kakakin Majalisar Dokoki, Shugaban Masu Rinjaye, Hon. Dabai, Shugaban Kwamitin Majalisar kan Harkokin Noma, Hon. Tunas Ingawa, wakilin Shugabannin Ƙananan Hukumomi, Shugaban Ƙaramar Hukumar Danja, Hon. Rabo Tanbaya, Babban Sakataren Ofishin Gwamna, Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, da sauran manyan ma'aikatan gwamnati.

   Salwa radio and television online media services Katsina..
Hakin mallaka MS Ingawa
SSA Media and Strategy
Government House, Katsina
September 18th, 2025

Post a Comment

Previous Post Next Post