Salwa RTV
Kaitsaye

Janar Junaidu Bindawa (RTD) Yazama Shugaban Hukumar Albashi Ta Kasa.


DAGA GIDAN GWAMNATIN JIHAR KATSINA
SANARWAR MANEMA LABARAI. 

Gwamna Radda Ya Taya Manjo Janar Junaidu Sani Bindawa (Rtd) Murnar Nada Shi Shugaban Hukumar Albashi da Kudin Shiga ta Kasa. 

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya taya Manjo Janar Junaidu Sani Bindawa (Mai Ritaya) murnar nadin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi masa a matsayin Shugaban Hukumar Albashi, Kudin Shiga da Tsarin Albashi ta Kasa (NSIWC).

Radda ya bayyana Janar Bindawa, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Bindawa, a matsayin gogaggen tsohon jami'in soja mai nagartaccen tarihin hidima ga ƙasa. 
Ya ce ƙwarewarsa, shugabancinsa da kishin ƙasa sun cancanci wannan muƙami.

Zaku Iya Tuna cewa Janar Bindawa na jagorantar Katsina State Community Watch Corps (CWC), inda yake taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa tsaron al'umma a faɗin jihar.

Ya yabawa Shugaba Tinubu bisa wannan naɗi, yana mai cewa hakan ya nuna an yaba da ƙwarewa, gaskiya da doguwar hidimar da Janar Bindawa ya yi wa Najeriya.

A ƙarshe, Gwamna Radda ya yi masa fatan alheri tare da addu'ar Allah Ya ba shi hikima da nasara wajen gudanar da sabon nauyin da aka ɗora masa.

Ibrahim Kaula Mohammed
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Katsina
21 ga Yuli, 2026
                   Wallafar Salwa Rtv Katsina.. 

Post a Comment

Previous Post Next Post