Inna Lillahi Wa Inna Illahi Rajiun
Yan Bindiga Sunkashe Abba
Cikin baƙin ciki da takaici muke sanar da rasuwar Abba, matashin nan da aka riƙa yawo da bidiyonsa ana dukansa dukan wulakanci.
Mutuwar ta zo ne bayan an tara kusan naira miliyan goma domin taimaka masa a matsayin kudin fansa. Daga baya Suka sanar da sun kashe shi.duk wasu labaran dake yawo cewa wai kakarsa taje domin kai kudin fansar amma suka nuna suna bukatar kari akan abinda suka bukata.
Wannan lamari yazama darasi mai nauyi ga al’ummar Arewa Musanmman Tallakawa.
Idan talaka ya yi shiru a kan zalunci, to gobe shi ne zai zama labari.
Idan shugabanni sun ɗauka babu abin da za mu iya, to mu tuna: Addu’a tana da ƙarfi, kuma zaɓinmu yana da tasiri lokacin zabe.
Allah Ka ji ƙan Abba, Ka gafarta masa, Ka kuma kyautata tamu bayan tafiyarsa.
Allah ya isa ga duk wanda ke da yanda zai Iya domin a kawo karshen wannan matsala yaki.
Allah 🙏 ya kawo mana karshen wannan masifa.
Salwa Rtv katsina reporting
Category
Labarai