Salwa RTV
Kaitsaye

Mutuwa Rigar Kowa..Ajali baya Jinkiri..

INNA LILLAHI WA'INNA ILAI HIR RAJU'UN, Allah ya yi ma Abubakar Yusuf Mati rasuwa bayan fama da doguwar jinya.

Marigayin, ɗa ne ga Yusuf Mati, tsohon ma’aikaci a gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), kamar yadda abokinsa Muhammad Kabir ya bayyana.

Za a gudanar da jana’izar marigayin da misalin karfe 3:00 na rana kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Muna rokon Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, tare da bai wa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.

Post a Comment

Previous Post Next Post