Innalillahi wa'inna Illahiraju'un Kai Jama'a
Barayi masu kwacen waya sun illata Marwan Usman mai kamfanin UK printing har wurin sana'ar shi a titin Ibb dake kofar kaura kusa da MTN office a daren jiya.
Kamar yadda muka yi magana dashi, ya shaida mani cewa barayin same shi ne a lokacin da yake kokarin zuba mai a generator domin cigaba da aiki a shagon shi kamar yadda ya saba aikin dare a wurin.
Lokacin da suka cimma shi sun nemi ya basu wayar salula dake hannun shi yace"ba zai bayar ba" haka suka cigaba da saran shi da makamai har suka ji mashi wannan ciwon,daga karshe dai basu samu nasarar tafiya da wayan ba.
Wannan lamari na kwacen waya da shiguwa a dauki mutane a cikin garin katsina fa yana ta kara ta,azzara,Allah ya kawo mamu mafita.
Salwa radio and television online media services Katsina.
Category
Labarai