Salwa RTV
Kaitsaye

Gomnan Kano Kuma Amirul hajji na Jihar kano ya Isa kasar Saudiyya.

Kai tsaye da kuke gani daga ƙasa mai tsarki, Yayin da Mai Girma Gwamnan jihar Kano kuma Amirul-Hajj na jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya isa Birnin makkah awannan rana ta Lahadi, inda tawagar Larabawa suke gaisawa da mai girma Gwamna kuma suke miƙa masa kyau ta musamman domin girmamawa da bayyana soyayya da ƙauna a gareshi.

Wannan lokaci mai girma zaɓaɓɓen Gwamnan Kano ya amshi lambar yabo ta musamman daga mahukunta da Larabawan kasar Saudiyya matsayin wadda ya jajirce ga maniyyatansa zuwa kasa mai tsarki domin gabatar da aikin hajji da sama musu ingantaccen yanayi da tsari da walwala domin aiwatar da ibada cikin Natsuwa. Madalla da gwamna Al'umma..

Engr Abubakar Iliyasu Haruna✍️📸
  Salwa radio and television 

Post a Comment

Previous Post Next Post